Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan bindiga sun sace Dalibai mata sama da 100 a Borno

Wasu gungun ‘Yan bindiga sun sace mata daliban makarantar Sakandare a garin Cibok da ke cikin Jahar Borno a yankin arewa maso gabacin Najeriya, kamar yadda Kwamishinan ‘Yan Sandan Jahar ya tabbatar. Kodayake Kwamishinan yace an sace daliban ne da suka je rubuta Jarabawa domin makarantun Jahohin Borno a rufe suke.

Wasu 'yan Maiduguri da ke juyayin hare haren bama bamai da Boko Haram ke kai wa a Najeriya
Wasu 'yan Maiduguri da ke juyayin hare haren bama bamai da Boko Haram ke kai wa a Najeriya Aminu Abubakar / Reuters
Talla

Kwamishinan yace an sace daliban ne da suka ce rubuta Jarabawa ne domin makarantun Borno a rufe suke.

Mazauna garin sun ce ‘Yan bindigan sun abka cikin makarantar ne a cikin motoci da babura a ranar Litinin kuma ana zargin mayakan Kungiyar Boko Haram ne da ke addabar yankin da hare hare.

Wani Jami’in Ma’aikatar Ilimi a Jahar Borno ya shaidawa Kamfanin dillacin labaran Faransa cewa akwai Sojoji da aka girke domin samar da tsaro a makarantar a lokacin da daliban ke rubuta Jarabawar amma kuma ‘Yan bindiga suka fi karfin Sojojin suka sace daliban.

Wata Majiyar tsaro a Najeriya tace Mata sama da 100 ne daliban makarantar Sakandare  ‘Yan bindiga suka sace. Majiyar tace daliban ba su kai 200 ba kamar yadda wasu kafofin yada labarai suka ruwaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.