Isa ga babban shafi
Masar

Masar: Kotu ta haramtawa ‘Yan uwa musulmi shiga zabe

Kotun kasar Masar ta haramtawa Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta Mohammed Morsi da Sojoji suka tumbuke shiga zabukan da za’a gudanar a kasar, kamar yadda kafafofin yada labaran kasar suka ruwaito.

Wasu magoya bayan hambararren shugaban Masar Mohamed Morsi, suna zanga-zanga a kasar Masar
Wasu magoya bayan hambararren shugaban Masar Mohamed Morsi, suna zanga-zanga a kasar Masar REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Tun lokacin da Sojoji suka tumbuke Morsi, gwamnatin da suka kafa ke ci gaba da karya Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi da ta jefa cikin jerin kungiyoyin ‘Yan ta’adda.

Kotun birnin Alexandria ce ta bayar da umurnin a haramtawa duk wani dan takara daga Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi shiga zaben shugaban kasa da na ‘Yan majalisu da za’a gudanar.

Wannan haramcin kuma ya zo bayan wasu gungun fararen hula sun shigar da bukatar a gaban kotun suna masu neman a haramta wa ‘Yan uwa Musulmi shiga zaben.

A watan Disemba ne gwamnatin Masar ta jefa kungiyar ‘Yan uwa musulmi cikin jerin kungiyoyin ‘Yan ta’adda wadanda gwamnatin ta zarga da kai wani munmunan hari a birnin al Kahira.

Janar Abuel Fattah al-Sisi wanda ya hambarar da Mohammed Morsi shugaban dimokuradiya na farko a Masar, ana ganin babu tantama shi zai lashe zaben shugaban kasa da za’a gudanar bayan ya tube kakinsa na Soji domin shiga takarar zaben da za’a gudanar a ranakun 26 zuwa 27 na watan Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.