Isa ga babban shafi
Najeriya

Kasashen duniya sun yi tir da harin da aka kai Abuja

Kasashen duniya sun yi tir da kuma Allah wadai dangane da mummunan harin da aka kai a birnin Abuja fadar gwamnatin Tarayyar Najeriya a jiya litinin. 

Tashar motar Nyaya
Tashar motar Nyaya EUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kasashen Amurka, Ingila, Faransa da kuma Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana harin a matsayin wani abin assha, yayin da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi alkawalin daukar dukkanin matakan da suka wajaba domin kare lafiyar al’umma tare da kawo karshen ayyukan ta’addanci a kasar.

Majiyar ‘yan sanda ta ce akalla mutane 71 ne suka rasa rayukansu a wannan hari da aka kai a tashar motar Nyanya da ke birnin na Abuja a daidai lokacin da jama’a ke kokarin zuwa wuraren ayyukansu.

Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta fito ta dauki nauyin kai wannan hari.

Wannan ne dai karo na 7 da ake kai hare-hare a birnin na Abuja daga lokacin da kungiyar Boko Haram ta soma gudanar da ayyukanta a kasar shekaru 4 da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.