Isa ga babban shafi
Guinea Bissau

Za’a yi zagaye na biyu a zaben G/Bissau duk da zargin Magudi

Hukumar zaben kasar Guinea Bissau ta saka ranar 22 ga watan gobe na Afrilu, domin gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu, tsakanin wanda yazo na farko tsohon Fira Minsita Carlos Gomes Junior na jam’iyya mai mulki, da kuma tsohon Shugaban kasar Kumbo Yala, wanda yazo na biyu.

Tsohon shugaban kasa Kumba Yalá, da Serifo Nhamadjo, da  Henrique Rosa
Tsohon shugaban kasa Kumba Yalá, da Serifo Nhamadjo, da Henrique Rosa Liliana Henriques/RFI
Talla

Tsohon Fira Ministan Gomes Junior ya samu kashi 48 cikin 100 a zagaye na farko, Inda Kumbo Yala ya samu kashi 23 cikin 100.

A wani labarin tsohon babban habsan sojan kasar, Janar Jose Zamora Induta, ya nemi mafaka a ofishin jakadanci Tarayyar Turai kwanaki bayan hallaka tsohon babban jami’in leken asirin kasar Samba Diallo ranar zabe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.