Senegal - 
Wallafa labari : Litinin 06 Feberairu 2012 - Bugawa ta karshe : Litinin 06 Feberairu 2012

Shugaba Wade na Senegal ya fara yakin neman zabe cikin rudani

Reuters/Gabriela Barnuaevo

Daga Suleiman Babayo

An kaddamar da yakin neman zaben Shugaban kasar Senegal da za a gudanar ranar 26 ga wannan wata na Febrairu.

Cikin makonnin da suka gabata an samu zanga zanga domin nuna adawa da shirin Shugaba Abdoulaye Wade dake neman wa’ani na uku na wasu shekaru biyar.
 

Tuni Shugaba Wade dan shekaru 85, ya yi watsi da matsin lambar kasashen duniya, inda ya ce 'yan Senegal ke da tacewa kuma su ake mulki. Amma matakin na Wade na sake takara a karo na uku, ya janyo suka da fusata daga kungiyoyin kare demokaradiya dana fararen hula.

Tuni ‘yan adawan kasar ta Senegal suka amince da shirin fahimtar juna domin kawar da Wade daga madafun iko, yayin da yake ci gaba da neman makalewa.
 

tags: Senegal
KAN MAUDU'I GUDA
Ra'ayoyi
Bada ra'ayi kan wannan magana
The content of this field is kept private and will not be shown publicly.
To prevent automated spam submissions leave this field empty.
CAPTCHA
This question is for testing whether you are a human visitor and to prevent automated spam submissions.
Image CAPTCHA
Enter the characters (without spaces) shown in the image.
Close