Masar - 
Wallafa labari : Juma'a 03 Feberairu 2012 - Bugawa ta karshe : Juma'a 03 Feberairu 2012

An sake samun mutuwar mutane biyu a Masar bayan Mutuwar 74

Masu Zanga-zanga a dandalin Tahrir na birnin Al Kahira a Masar.
Masu Zanga-zanga a dandalin Tahrir na birnin Al Kahira a Masar.
REUTERS/Asmaa Waguih

Daga Awwal Ahmad Janyau

mutane biyu sun rasa ransu, sama da mutane 400 kuma sun jikkata sanadiyar wata sabuwar zanga-zanga da ta barke bayan mutuwar mutane 74 a filin wasan kwallon kafa tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar Al masry da Al Ahly a birnin Port Said na kasar Masar.

Mutanen biyu sun mutu ne bayan da ‘yan sanda suka harba harsashe domin tarwatsa gangamin mutane a birnin Suez.

Haka zalika, a Birnin Alkahira daruruwan masu zanga-zanga ne ci gaba da yin gangami a saman titi bayan arangama da ‘yan Sanda.

A birnin Port Said ne za’a yi janai’zar wadanda suka mutu sanadiyar rikicin kwallon kafa a ranar Laraba.

An samu mutuwar rayukan ne sanadiyar rikici tsakanin magoya bayan manyan kungiyoyin kwallon kafar kasar Al Ahly da Al Masry a birnin Port Said.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon ya bukaci mahukuntan Masar Daukar matakai game da rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 74 a fiilin wasan kwallon kafa.

Kakakin Ban Ki-moon yace sakataren Majalisar ya kadu matuka, bayan samun rikicin tsakanin magoya bayan kungiyar al Masri da Al Ahly a birnin Port Said, rikicin da ya jikkata darurua da dama.

Hukumar FIFA da ke kula da kwallon kafa a duniya, ta bukaci mahukuntan Masar gabatar mata da cikakken Rehoton rikicin wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 74

A cewar FIFA ko wace gasa akwai sharuddan da aka shata, amma hukumar ta bukaci cikakken bayani domin diba faruwar al’amarin.

Tuni dai Sepp Blatter ya danganta wannan hasarar rayukan a matsayin ranar bakin ciki ga kwallon kafa.

Yanzu haka kuma a kasar Masar an fara zaman Makoki na kwanaki uku

Haka kuma hukumar CAF dake kula da kwallon kafa a Afrika, tace a wasannin cin kofin Afrika da ake ci gaba da gudanarwa a kasashen Gabon da E/Guinea, kafin fara wasannin a karshen makon nan, za’a kebe minti daya domin juyayin wadanda suka mutu da jikkata a rikicin na Masar.

Shugaban hukumar ne Isa Hayatu ya bada wannan sanarwar.

A yau Juma’a ne kuma hukumar kwallon kafar yankin kasashen Asia ta mika sakon ta’aziyarta ga mamatan da suka mutu a masar.

Tuni dai Fira ministan kasar Masar Kamal al-Ganzuri ya sanar da sallamar shugabannin kwallon kafar kasar sanadiyar tashin hankali, tuni kuma Gwamnan Port Said ya ajiye aikinsa bayan samun wannan rikicin.

 

tags: Kwallon Kafa - Majalisar Dinkin Duniya - Masar
KAN MAUDU'I GUDA
Ra'ayoyi
Bada ra'ayi kan wannan magana
The content of this field is kept private and will not be shown publicly.
To prevent automated spam submissions leave this field empty.
CAPTCHA
This question is for testing whether you are a human visitor and to prevent automated spam submissions.
Image CAPTCHA
Enter the characters (without spaces) shown in the image.
Close