Kwallon Kafa - Wallafawa ta karshe : 30/01/12
2012: Gasar Cin Kofin Afrika
Kofin Zinari na gasar Afrika ta CAF

A ranar 21 ga watan Janairu ne aka fara gudanar da gasar cin kofin Afrika a kasashen Gabon da Equatorial Guinea, inda kasashen Afrika 16 zasu haska a gasar, kuma wannan ita ce gasa mafi girma a Nahiyar Afrika. An fara gudanar da gasar ne a Shekarar 1957. Wannan gasa ana shirya ta ne domin kara dankon zumunci da soyayya tsakanin kasashen Afrika, kuma gasa ce da ake bajakolin ‘yan wasan Afrika, inda kungiyoyin kwallon kafa a duniya ke bude idonsu domin cefanen ‘yan wasa.

 
Rashidi Yekini na Najeriya ya mutu yana da shekaru 48
07/05/2012 - Wasanni

Rashidi Yekini na Najeriya ya mutu yana da shekaru 48

Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yi bayani ne game da Rashidi Yakini tsohon dan wasan Super Eagle a Najeriya wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Juma’a 4 ga watan Mayu yana da shekaru 48 bayan kwashe lokaci yana jinyar rashin lafiya.

Mazan jiya Roger Milla abokan wasan shi suna taya shi murnr zira kwallo a raga a lokacin da yake taka kwallo a Kamaru
20/04/2012 - Kamaru

Roger Milla zai kalubalanci Hukumar Kwallon Kamaru

Roger Milla tsohon fitaccen dan wasa kasar Kamaru ya bayyana damuwar shi game da rashin tsallakewar kasar Kamaru zuwa gasar cin kofin Afrika da aka kammala a kasashen Gabon da Equatorial Guinea, ...

Matsalolin Nijar da Najeriya a kwallon kafa
20/02/2012 - Wasanni

Matsalolin Nijar da Najeriya a kwallon kafa

A cikin shirin, mun diba irin matsalolin da suka shafi Tawagar ‘Yan wasan Mena a gasar cin kofin Åfrika da aka kammala a kasashen Gabon da Equatorial Guinea da irin matsalolin da suka shafi kwallon kafa a Najeriya da sabbin sauye sauye da kasar ke yi domin kaucewa bacin rana.

'Yan wasan kasar Zambia da suka lashe kofin Africa
16/02/2012 - Kwallon kafa

Zambia ta dawo matsayi na 28 a duniya bayan lashe kofin Africa

Kasar Zambia da ta lashe gasar cin kofin Afrika ta dawo matsayi na 28 a duniya daga matsayi na 43 Amma matsayi na hudu a Afrka. Kasar Cote d’Ivoire ce a matsayi na daya a Afrika wacce ta buga wasan karshe da Zambia a gasar cin kofin Afrika da aka kammala a Gabon da Equatorial Guinea Amma matsayi na 15 a duniya.

Stephen Keshi, Kocin Super Eagles na Najeriya
15/02/2012 - Kwallon kafa

Keshi zai yi amfani da matasa a wasan Najeriya da Liberia

A yau ne Najeriya zata buga wasan sada zumunci da kasar Liberia a birnin Manrovia, Stephen Keshi ya bayyana ‘Yan wasa Ashirin da zasu bugawa Najeriya wasan kuma dukkanin ‘yan wasa ne masu taka leda a gida.

'Yan sanda suna kokarin kare daruruwan mutane 'Yan kasar zambia da suka zo filin saukar jirgin Lusaka domin tarbar 'Yan wasan da suka lashe kofin Afrika
14/02/2012 - Kwallon kafa

Daruruwan ‘Yan zambia ne suka Tarbi ‘Yan wasan Copper bullet

Dubun dubatar ‘Yan kasar Zambia ne suka yi dandazo domin tarbar ‘yan wasan Copper Bullet wadanda suka lashe gasar cin kofin Afrika a karshen mako bayan Doke kasar Cote d'Ivoire a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

'Yan wasan kasar Zambia lokacin da suke lashe kofin gasar cin kofin Afrika na bana.
13/02/2012 - Zambia

Zambia ta lashe kofin Afrika

Kasar Zambiya ta lashe gasar cin kofin Afrika  bayan doke Cote d'Ivoire ci 8-7 a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Wannan ne karo na farko da Zambia ta samu nasarar lashe kofin gasar bayan zuwa na biyu a shekarar 1974 da 1994.

Zambia ta lashe kofin Afrika bayan Doke Cote d'Ivoire
13/02/2012 - Wasanni

Zambia ta lashe kofin Afrika bayan Doke Cote d'Ivoire

Kasar Zambiya ta lashe kofin gasar cin kofin Afrika karo na farko bayan doke Cote d voire ci 8-7 a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Wannan ne karo na farko da Zambia ta samu nasarar lashe kofin gasar bayan zuwa na biyu a shekarar 1974 da 1994.

Sakamakon Wasanni
Duniyar Wasanni
Gasar Cin kofin Afrika: Senegal ta fice, Equatorial Guinea da Zambia sun Tsallake Quarter Final
 
30/01/2012
by Awwal Ahmad Janyau
 
 
Shirin Wasanni game da Gasar Cin kofin Afrika
Wasanni: Gasar Cin kofin Afrika
 
23/01/2012
by Awwal Ahmad Janyau
 
 
Tsokaci game da Gasar Cin kofin Afrika
Duniyarmu A yau: Gasar Cin kofin Afrika
 
23/01/2012
by Bashir Ibrahim Idris
 
 
Close