Isa ga babban shafi
Mali

Gurbacewar lamarin tsaro kan iyakar kasar Mali da ta jumhuriyar Nijar

Makiyaya ‘yan karkara guda 50 ne su ka rasa rayukansu a yammacin kasar Nijar a cikin yan shekaru na baya-bayanan .Wanan lamari ya wakana ne sanadiyar harin da wasu ‘yan bindiga su ka rika kawowa daga kasar Mali mai iyaka da kasar ta Nijar.A cikin shekara guda, an kawo hare-hare guda 27 a yankin Ouallam da ke iyaka da kasar ta Mali.Hari na baya-bayanan da aka kawo,wasu yan kabilar Abzinawa ne da ake kira Daoussahak da ke kan babur su ka kawoshi. Makiyaya guda 22 ne su ka rasa rayukansu sanadiyar wanan lamari a cikin watan Aprilun da ya gabata kamar yada wakillan makiyayen su ka sanar.Bayan sace-sacen dabobi, yankin na fama da hare-hare na kungiyar Aqmi wato kungiyar al’Qaida a yankin yammacin Afrika . 

Jami'an tsaro a kasar jumhuriyar Nijar
Jami'an tsaro a kasar jumhuriyar Nijar ISSOUF SANOGO / AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.