Kididiga kan zaben shugaban kasa a jumhuriyar Nijar

Wani kanfani da ake kira Omega Intelligency, da ya kware wajen bincike ,lissafi da kididiga,ya gano da cewa a zaben shugaban kasa da zai gudana a kasar jumhuriyar Nijar,Mahamadou Issoufou na jama’iyar PNDS -Tarrayar zai kassance na Farko da yawan kuri’u kishi 46 cikin dari,Mahamane Ousman na CDS-Rahama na 2 da yawan kuri’u kishi 26 cikin dari,a yayin da Cheiffou Amadou na RSD-Gaskiya zai kassance na 3 da yawan kuri’u kishi 24 cikin dari.
Binciken ya nuna da cewa Cheiffou Amadou zai taka rawa ta massanman kan ganin wanda zai kassance shugaban kasar Nijar a shekara ta 2011.
Kanfanin na Omega mai cibiya a binin Yamai na jumhuriyar Nijar ,ya gudanar da wanan bincike ne ta hanyar kira kuma jin ra’ayin jama’a ta waya, kwanaki 40 kaffin ranar zabe.

Delicious
Digg
Facebook
Twitter
Yahoo!
Technorati



