Hukumar Ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya, tace dole sai kasashen Afrika sun magance matsalar yunwa da ke addabar kasashe 27 a nahiyar kafin kasancewa matsayin Yankin da ya samu ci gaba.
Wata Kungiyar fararen hula a Jamhuriyar Nijar, ta bukaci kamfanin Areva, mallakar kasar Faransa, da ke hako ma’adinin uranium a kasar, biyan kudaden Diyya ga ‘Yan Nijar dai dai da yadda Kamfanin ke biyan Faransawan da suka mutu.
Gwamnatin Najeriya tace zata girke dakarunta a kasar Guinea Bissau don taimakawa kasar komawa ga mulkin fararen hula, kamar yadda kungiyar ECOWAS ta bukata.
Hukumomin Kasar Uganda sun ce, sun yi nasarar kama Caeser Acellam wani babban kusa a kungiyar ‘Yan Tawayen Lords Resistence Army, da ke karkashin Joseph Kony. Kakakin rundunar sojin Uganda, Lt Col Felix Kulayigye, yace Acellam ne jami’I na hudu a kungiyar ‘Yan Tawayen, bayan Joseph Kony, da Dominic Ongwen da Okot Odhiambo.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya bukaci Sudan ta janye dakarun ta daga Yankin Abyei da ake takaddama akai. Ban wanda yake jawabi bayan ficewar dakarun Sudan ta kudu, ya bukaci kasashen biyu su mutunta yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.
A Yau Litinin ne Manyan Hafsoshin sojin kasashen Afrika ta Yamma zasu gudanar da wani taro a Abuja babban birnin Najeriya, don nazarin hanyoyin da zasu bi wajen girke dakaru a kasar Guinea Bissau da Mali.
A yau juma’a shugaban kasar Senegal Macky Sally a buda soma wani gawurtacen bikin al’adu na kirkire kirkiren ayukan hanu na nahiyar Afrika a birnin Dakar babban birnin kasar ta Senegal (Dak’Art).
Jamiyar RCD da ta kauracewa zaben yan majalisar dokokin da aka gudanar a jiya alhamis a kasar Aljeriya, ta kalubalanci sakamakon da gwamnatin kasar ta bayar, kan yawan jama’ar da suka halarci zaben na kashi 42,9%, inda ta ce sakamakon bai wuce kashi 18% ba, kamar yadda shugaban jami’iyar Mohcin Bellabas ya sanar.
A wata ziyara da kai kasar Cote d’Ivoire, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, yace kungiyar kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, zata tura wata tawaga zuwa kasar Guinea Bissau don tattaunawa da sojojin kasar, domin ganin sun mayar da kundin tsarin mulki.
Al’ummar Algeria sun fara kada kuri’arsu a zaben farko na ‘Yan Majalisu tun fara zanga-zangar kasashen Larabawa, inda Jam’iyyar Mai mulki da Jam’iyyar ‘yan uwa musulmi ke fatar samun rinjayen kujeru tsakanin Jam’iyyu 44 da suka shiga takarar zaben ‘Yan Majalisa 462.
Manyan Jami’an tsaron kasashen da ke raya tafkin Chadi, sun gudanar da taro a Jamhuriyar Nijar, don nazarin hanyoyin da zasu dakile safarar makamai da kuma ayyukan ta’adanci domin samun ci gaban kasashensu.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi watsi da rahotan kungiyar agaji ta Save the Children, wanda yace mata na fama da tsananin wahala wajen haihuwa da kuma renon kananan yara, abinda ya sa kasar ta zama ta karshe a mizanin kasashen duniya 165.
A kasar Libya mutane da dama sun samu rauni tare da samun mutuwar mutum daya sakamakon musayar wuta da aka yi tsakanin Jami’an tsaro da ‘Yan bindiga dwadanda suka yi zanga zanga a Hedikwatar Gwamnati a Birnin Tripoli.
Gwamnatin Jahar Flato a Najeriya ta sanar da haramta yin Acaba da babura a birnin Jos da kewaye, saboda yunkurin dakile ayyukan laifi da ake da baburan, kamar yadda ta sanar bayan taron Majalisar ...
Babban mai gabatar da kara a shari’ar Charles Taylor tsohon shugaban kasar Liberia, ya nemi a daure tsohon shugaban shekaru 80 a gidan yari bayan kama shi da laifin aikata laifukan yaki a Saliyo.
Dakarun Sojan kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, sun ce sun isa, zuwa maboyar gudajjen janar din sojan kasar Jean Bosco Ntaganda, da ake zargi da haddasa tashin hankalin da ya yi sanadiyyar dubun dubatan mutane rasa gidajensu.
‘Yar marigayi Moammar Gaddafi na kasar Libya, Aisha Gaddafi ta nanata bukatar ganin Hukumomin fadin duniya sun tallafa mata tilasta binciken yadda aka kashe mahaifinta da wani dan-uwanta ...